Isa ga babban shafi
Najeriya

Masari ya yi barazanar gurfanar da hukumar Kwastam kan kashe-kashe a Katsina

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari yayi barazanar gurfanar da hukumar Kwastam a gaban kotu, bayan da wasu jami’anta suka kashe mutane 10 a garin Jibiya, ranar 9 ga watan Agustan da muke.

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari.
Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari. © The Guardian Nigeria
Talla

Cikin sanarwar da ya fitar ta hannun daraktansa na watsa labarai, Abdu-Labaran Malumfashi, gwamnan ya yi A-wadai da yawaitar kashe mazauna jihar da jami’an hukumar Kwastam ke yi a jihar ta hanyar tukin ganganci musamman a yankin Jibiya da ke kan iyaka, da sunan hana fasakaurin shinkafar kasashen ketare.

Masari yayi gargadin cewar gwamnatinsa ba za ta sake yarda da irin wannan lamari ba, zalika yana nazarin maka Hukumar Kwastam din Najeriya a kotu domin hakan ya zama matakin hana sake faruwar gangancin da jami’anta ke yi a jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.