Isa ga babban shafi
Najeriya - Katsina

'Yan sanda sun dakile yunkurin satar mutane a Katsina

Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina dake arewacin Najeriya ta samu nasarar dakile yunkurin wani gungun bindiga na sace mutane a kauyen Karijam dake karamar hukumar Dandume.

Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya.
Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya. AFP/File
Talla

Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun afkawa yankin na Dandume ne a daren ranar Alhamis inda nan take suka fara harbe-harbe, sai dai hakarsu ba ta cimma ruwa ba saboda daukin da ‘yan sanda suka kai tare da samun nasarar ceto mutane 9 da maharan suka yi yunkurin yin awon gaba dasu.

Cikin sanarwar da ya fitar kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar ta Katsina SP Gambo Isah ya ce sun samu nasarar dakile muguwar aniyar ‘yan bindigar ne ta hanyar yi musu kwanton Bauna a wani yanki na karamar hukumar Sabuwa, akan hanyar da suka shirya bi domin tserewa da mutanen da suka yi yunkurin sacewa.

Sanarwar ta ce bayan fafatawa na wani lokaci maharan sun tsere tare da raunukan harbi, inda suka yada wayoyin hannu da kayayyakin abincin da suka sace daga hannun mutanen da suka afkawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.