Kotun ECOWAS ta bukaci Najeriya ta biya wani dan jarida diyyar miliyan 30
Kotun ECOWAS da ke zamanta a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ta bukaci gwamnatin Tarayya da jihar Cross River da su biya dan jarida Agba Jalingo Naira miliyan 30 a matsayin diyya, sakamkon tsare shi ba bisa ka’ida ba, da kuma azabtar da shi.
Wallafawa ranar:
A wani hukunci da mambobin alkalai uku suka gabatar ranar Jumma'a karkashin jagorancin shugaban kotun, mai shara’a Edward Amoako Asante, sun ce gwamnatin Najeriya ta sabawa tanade-tanaden ka'idojin adalci na duniya, musamman, Yarjejeniyar Afirka kan kare hakkin Dan Adam, wanda Nijeriya ta sanya hanu.
A cewar kotun, “An kama Agba Jalingo kuma an daure shi da mari har na tsawon kwanaki 34 ba tare da gurfanar da shi a gaban kotu ba. Abin da ke tabbatar da take hakkokinsa da cin zarafinsa.
Kungiyar SERAP ta shigar da kara a madadin dan jaridar, biyo bayan kamun da aka yi wa Jalingo a ranar 22 ga watan Agustan shekarar 2019 bayan da ya wallafa wani labari a jaridar sa ta yanar gizo, ‘Cross River Watch,’ da ke cewa Gwamna Ben Ayade ya karkatar da N500m na jihar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu