Isa ga babban shafi
Najeriya-Demokradiyya

Buhari ya sha alwashin mutunta umarnin Kotu tare da baiwa 'yan jarida 'yanci

Cikin kalamansa na ranar Demokradiyya shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin girmama bangaren shari’a tare da bayar da cikakkiyar damar ‘yancin fadan albarkacin baki ga kafafen yada labarai.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Solacebase
Talla

Shugaba Buhari wanda gwamnatinsa ke ci gaba da shan suka kan rawar da ta ke takawa wajen kin mutunta umarnin kotu a lamurra da dama, ya ce na aikin tukuru don tabbatar da ‘yancin kafafen yada labarai tare kuma da biyayya sau da kafa ga umarnin kotu.

Yayin jawabin na shugaba Muhammadu Buhari a bikin sabuwar ranar Demokradiyyar kasar, ya bayyana irin nasarorin da gwamnatinsa mai shekaru 5 a karagar mulki ta samu duk kuwa da yadda bayanai ke nuna tabarbarewar tattalin arziki karancin tsaro da kuma karuwar marasa aikinyi a sassan Najeriyar mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar Afrika.

A cewar shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari akwai alaka mai karfi tsakanin bangaren yada labarai da duk wata gwamnati da ke fatan kaiwa ga nasara, sai dai ya koka da yadda wasu kafafen yada labaran kan wuce makadi da rawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.