Isa ga babban shafi
Najeriya

Takaicencen tarihin Farouk Yahaya sabon babban hafsan sojin kasan Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada sabon Babban hafsan Sojojojin kasa, domin maye gurbin Laftaal Janar Attahiru Ibrahim Wanda Allah ya yi wa rasuwa a makon jiya sanadiyar hadarin jirgin sama

Sabon babban Hafson Sojin kasa na Najeriya, Manjo Janar Farouk Yahya.
Sabon babban Hafson Sojin kasa na Najeriya, Manjo Janar Farouk Yahya. © Nigeria defence ministry
Talla

An haifi sabon shugaban rundunar Sojan kasar Manjo Janar Faruku Yahaya a garin Sifawa dake karamar hukumar Bodinga a Jahar Sokoto a ranar 5, ga watan Janairu 1966.

Ya samu gurbin karatu a kwalejin horar da kananan hafsoshin Soja ta NDA a rana 27 ga watan Satunbar shekarar 1985, inda ya kuma kamala a watan Satunbar 1990.

Janar Yahaya ya rike Mukamai daban daban da suka hada da, shugaban Runduar dake gadin shugaban kasa,  Darakta a Kwalejin horas da manyan hafsoshin soja dake jaji.

Yahaya ya rike  Babban jam’in gudanar da ayukan Soja a Hekwatar soja ta kasa, ya zamo shugaban ma'aikatan a wata runduna ta Musaman "Opretion Pulo Shield".

Kana ya zamo baban Jami’in Soja a ofishin Ministan tsaro kafin kuma ya zamo baban Kwamandar Runduna ta hudu, da shugaban rundunar yaki da ta’addanci ta zaman lafiya dole.

Ya rike shugaban sashin samar da horo na rundunar sojan kasa, kuma ya zamo baban sakataren rundunar soja na kasa. Ya kuma jagoranci runduna ta daya a matsayin GOC. Kafin turashi Maiduguri inda ya zamo shugaban rundunar hadin kai har zuwa lokacin wanan nadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.