Isa ga babban shafi
Najeriya-Buhari

Buhari ya nada sabon shugaban rundunar Sojin kasa ta Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Farouk Yahya a matsayin sabon shugaban rundunar sojin kasa domin maye gurbin Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da ya rasu a hadarin jirgin sama a makon jiya.

Sabon babban Hafson Sojin kasa na Najeriya, Manjo Janar Farouk Yahya.
Sabon babban Hafson Sojin kasa na Najeriya, Manjo Janar Farouk Yahya. © Nigeria defence ministry
Talla

Daraktan yada labaran ma’aikatarn tsaron kasar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya sanar da cewar kafin nadin Janar Yahya ya rike mukaman da suka hada da Babban kwamanda runduna ta daya ta sojin Najeriya dake Kaduna da kuma shugaban rundunar yaki da ta’addanci da aka yiwa suna ‘Operation Hadin Kai’ da ke yaki da kungiyar book haram a Maiduguri.

Wannan nadin ya kawo karshen cece kucen da ya biyo bayan wanda ake zaton shugaban kasa Muhammadu Buhari zai zaba domin jagorancin rundunar sojin kasa a daidai lokacin da kasar ke fama da yaki da ta’addanci da kuma tashe tashen hankula a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.