Isa ga babban shafi
Najeriya

Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziya ga iyalan Babban hafsan sojan Najeriya

Uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan Babban hafsan sojan Najeriya Janar Ibrahim Attahiru da ya rasu ranar Jumma’a sakamakon hadarin jirgin sama.

Uwargidan shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari lokacin ziyarar jaje da ta kai ga iyale Babban hafsan sojin Najeriya Janar Ibrahim Attahiru da ya rasu a hadarin jirgin sama. 23 ga watan Mayun 2021.
Uwargidan shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari lokacin ziyarar jaje da ta kai ga iyale Babban hafsan sojin Najeriya Janar Ibrahim Attahiru da ya rasu a hadarin jirgin sama. 23 ga watan Mayun 2021. © Aisha Buhari Twitter
Talla

Ta shafin ta na Twitta uwargidan shugban kasa, Aisha Buhari ta bayyana kai ziyarar ta’aziyar tare da wallafa hotunan ziyarar.

Aisha Buhari ta ziyarci iyalan Babban hafsan sojan Najeriya

A ranar Asabar aka binne Babban Hafsan sojan tare da sojoji 10 da suka mutu a hatsarin jirgin sama a Kaduna.

Aisha Buhari ta ce rasuwar babban hafsan sojin babban rashi ne ga iyalansa da kuma Najeriya baki ɗaya.

Rahin halartan shugaban kasa da mataimakin sa jana'iza

‘Yan Najeriya sun soki shugaban kasa da mataimakinsa kan rashin halartan jana’izan babban hafsan sojin Najeriyar da wasu mukarrabansa da akayi a Abuja.

Yayin da wasu sukayiwa Ministan tsaro Abubakar Malami da wasu gwamnonin jihohin kasar ca kan zabin halartan bukin aure maimakon karrama manyan sojojin da suka rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.