Burina shi ne ganin jiragen kasa na zirga zirga - Soyinka
Fitaccen marubucin Najeriya Farfesa Wole Soyinka yayi watsi da masu sukar gwamnatin kasar kan cewar ta cika ciwo bashi domin gudanar da manyan ayyuka cikinsu har da gina hanyoyin jiragen kasa da kuma sayo taragansu.
Wallafawa ranar:
Soyinka wanda yace shi abinda yake son gani shine jiragen kasa suna zirga zirga a fadin Najeriya saboda muhimmancin su, yayi watsi da masu kukan bashin da ake ciwowa domin gudanar da ayyukan.
Fitaccen marubucin yace babu dalilin cigaba da mahawara kan bashin da Najeriya ke karbowa daga China domin wadannan ayyukan, inda yace aikin Majalisa ce ta duba ta kuma tantance da kuma Nazari kan yadda za’a biya bashin.
Soyinka yace yana matukar bukatar ganin jiragen kasa na zirga zirga, domin ya girma yana ganin su, saboda haka yanzu lokaci ne na sake dawowar su.
Marubucin yace bai dace mutane su bari yarjejeniyar biyan bashin ta razana su ba, domin hurumin da ya rataya akan masana tattalin arziki da kuma Babban Bankin Najeriya kenan, tare da hukumomin dake kula da ciwo bashin da kuma Majalisar Dattawa.
Farfesa Soyinka ya baiwa gwamnati shawarar cewar kada tayi watsi da tsaffin layin jiragen da ake da su, domin ana iya amfani da su wajen safarar shanu da kuma baiwa makiyaya tsaron da ta dace.
Marubucin yace ya dace jami’an tsaron dauke da makamai su yiwa makiyaya dake safarar shannun rakiya maimakon barin Fulani makiyayan suna daukar bindiga kirar AK47.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu