Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane da dama jirgin kasa ya danne a Jebba

Rahotanni daga Jebba dake Jihar Niger ta Najeriya na cewa, kawo yanzu ba a san hakikanin  adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba sakamakon hatsarin jirgin kasa, kuma ya zuwa a yammacin jiya ba a fara aikin agaji don zakulo mutanen da taragun jirgin ya danne ba. 

Hatsarin jirgin ya haddasa arasar rayukan jama'a da dama kamar yadda mazauna Jebba suka tabbatar
Hatsarin jirgin ya haddasa arasar rayukan jama'a da dama kamar yadda mazauna Jebba suka tabbatar naijadetails.com
Talla

A hirarsa da sashen hausa na rfi, sarkin Jabba ya bayyana ce wa, har yanzu ana iya ganin hannaye da kafafuwan mutanen da jirgin ya danne bayan ya yi hatsari tun a ranar Asabar din da ta gabata.

Sarkin ya ce, akwai wadanda kawunansu suka fita bayan jirgin ya fado mu su.

Sannan ya ce, kawo yanzu ba a san adadin mutanen da jirgin ya danne ba, har sai an kammala aikin janye jirgin.

Ga dai cikakken bayanin da ya yi mana.

01:18

Bayanin Sarkin Jebba kan hatsarin jirgin kasa

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki, ya aike da sakon ta'aziya ga iyalan wadanda hatsarin ya ritsa da su, yayin da ya bayyana kaduwarsa da aukuwar lamarin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.