Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara

Ba a jihar mu aka fara satar dalibai ba - 'Yan Majalisar Zamfara

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara dake Najeriya tayi watsi da umurnin gwamnatin kasar na sanya dokar hana shawagin jiragen sama a Jihar da kuma haramta hakar ma’adinai.

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle
Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle © Twitter / @Bellomatawalle1
Talla

Yayin zaman da Majalisar tayi kann wannan batu, Majalisar dokokin ta kada kuri’ar yankan kauna akan Mai Baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Manguno saboda abinda suka kira ‘nuna halin ko in kula’ kan matsalolin tsaron da suka addabi Jihar ta su.

Daukar wannan mataki ya biyo bayan kudirin da Dan Majalisa Faruk Dosara ya gabatar wanda ke zargin hukumomin tsaron Najeriya da gazawa wajen kaiwa jama’a dauki lokacin da ake kai musu hari.

Satar Dalibai

Dosara yace babu dalilin kafa dokar hana shawagin jiragen sama a jihar, domin ba a jihar Zamfara aka fara sace daliban makarantu ba, inda yake cewa anyi a Chibok da Dapchi da Kankara da kuma Kagara amma gwamnatin Buhari bata dauki irin wannan mataki ba.

Wasu daliban makarantar sakandaren 'yammata ta Jengebe dake jihar Zamfara, yayin murnar komawa ga iyayensu.
Wasu daliban makarantar sakandaren 'yammata ta Jengebe dake jihar Zamfara, yayin murnar komawa ga iyayensu. AP - Sunday Alamba

Mai Magana da yawun Majalisar Mustapha Kaura yace kudirin yayi kuma suka kan yadda hukumomin tsaro ke tattara bayanan asiri da kuma musayar su a tsakanin su.

Majalisar ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta kafa wani kwamiti mai karfi da zai gudanar da bincike da kuma sake fasalin hukumomin tsaron kasar kan yadda suke aiki a Jihar, yayin da tayi kira ga gwamnatin jihar da gudanar da bincike kan mutanen da ake zargi suna yiwa harkokin tsaro zagon kasa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.