Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara

Gwamnatin Zamfara ta sanar da nasarar ceto daliban Sakandiren Jengebe 279

Rahotanni daga Najeriya sun ce anyi nasarar ceto dalibai ‘yammatan sakandiren Jangebe 279 wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su tun a makon jiya, bayan shiga tsakanin da tubabbun ‘yan bindigar jihar ta Zamfara suka yi a tattaunawa da masu garkuwar wanda ya kai ga nasarar tseratar da su.

Daliban Sakandiren Jengebe ta Jihar Zamfara kenan bayan nasarar ceto su daga hannun 'yan bindigar da suka yi garkuwa da su a makon jiya.
Daliban Sakandiren Jengebe ta Jihar Zamfara kenan bayan nasarar ceto su daga hannun 'yan bindigar da suka yi garkuwa da su a makon jiya. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE
Talla

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle wanda ya karbi tawagar daliban da safiyar yau Talata, ya ce an yi nasarar cimma jituwa da ‘yan bindigar tun a jiya Litinin inda suka bayar da ‘yammatan da misalin karfe 4 na yammaci.

A cewar Gwamna Matawalle ilahirin daliban an gudanar musu da gwaje-gwajen lafiya yayinda aka ciyar da su sinadaran abinci masu gina jiki don murmurowa daga bakar wahalar da suka sha, gabanin kawo su fadar gwamnati a safiyar yau Talata.

Gwamnan a jawabinsa ya ce nasarar ceto ‘yammatan ba tare da biyan ko sisi ba, alamu ne da ke kunyata masu kwaroroton babu tsaro a Najeriya.

Majiyar fadar gwamnatin Zamfara ta ce  da misalin karfe 5 na asubahin yau ‘yammatan 279 suka isa fadar gwamnatin Gusau, don ganawa da Gwamnan gabanin sada su da ahalinsu.

Gwamnan na Zamfara ya yi kira ga iyaye kan kada abin da ya faru ya razana su wajen cire ‘ya’yansu daga makarantar ta Jangebe yana mai shan alwashin kara matakan tsaro don bayar da cikakkiyar kariya ga rayuka da lafiyar al’ummar da ke cikin makarantar.

Haka zalika gwamnan ya taya iyaye da ilahirin al’ummar Jihar da na Najeriyar murnar nasarar kubutar da daliban lafiya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.