Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta haramta shawagin jiragen sama a sararin samaniyar Zamfara

Gwamnatin Najeriya ta dauki matakin haramta shawagin jiragen sama a sararin samaniyar jihar Zamfara baya ga dakatar da harkokin hakar zinaren da ke gudana ba bisa ka’ida ba a wani yunkuri na kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane wanda ke ci gaba da tsananta a jihar.

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari. © Presidency of Nigeria
Talla

Majiyar fadar shugaban Najeriya da ke tabbatar da matakin ta ce ta hakan ne za a kawo karshen musayar da ‘yan bindiga ke yi da zinaren don karbar makamai.

Wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnatin Najeriyar ke haramta hakar zinaren ba bisa ka’ida ba don yaki da ayyukan masu garkuwar da kuma kai hare-haren babu gaira babu dalili, said ai wannan ne karon farko da gwamnatin ke haramta shawagin jiragen.

Masharhanta al’amuran tsaro a Najeriyar na alakanta haramta shawagin jiragen a Zamfara da zarge-zargen da suka tsananta wanda ke nuna cewa akwai jiragen da ke kai wa ‘yan bindigar makamai a asirce, zargin da gwamnati da dakarunta suka jima suna musantawa.

A shekarun baya-bayan nan ne ‘yan bindiga suka tsananta kai hare-hare sassan jihar ta Zamfara tare da hallaka tarin jama’a baya ga sace dubunnan jama’a don karbar fansa ciki har da daliban Sakandiren gwamnati ta Jangebe kusan 300 a baya-bayan da aka ceto jiya Talata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.