Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Rikici tsakanin 'yan bindiga a Katsina ya lakume rayuka

A Najeriyar Rahotanni daga jihar Sokoto sun ce an yi kazamin fada tsakanin wasu kungiyoyin ‘yan bindiga a garin illela dake karamar hukumar Safana, inda da dama suka rasa rayukansu wasu gwammai kuma suka jikkata.

Misalin 'yan bindiga da ke addamar al'umma a sassan Najeriya.
Misalin 'yan bindiga da ke addamar al'umma a sassan Najeriya. Daily Post
Talla

Bayanai sun ce an gwabza fadan ne tsakanin kuniyar ‘yan bindiga na Mani Sarki da ake kyautata zaton sun karbi tayin gwamnati na sulhu da kuma bangaren wani Dankarami, kawo yanzu dai babu karin bayani kan adadin wadanda suka mutu da kuma wadanda suka jikkata.

Rahotanni sun ce bayan sarki ya karbi tayin gwamnati na sulhu ne ya koma Illela da zama don ci gaba da sabuwar rayuwa, amma wasu daga cikin yaransa suka ki karbar haka.

Biyo bayan haka ne wasu ‘yan bindiga karkashinn jagorancin wani da ake kira Alhaji Dankarami sun kai hari garin na Illela, amma bangaren Mani suka taka musu birki, suka raba su da makamansa masu tarin yawa, hakan ya harzuka ‘yan bindiga da suka ki tuba.

Abu na biyu da ake zaton ya kawo rikicin, shine, wani kani ga Sarki Mani, ya taba sace matar daya daga cikin yaran wani dan bindiga da ake kira Dangwate har sai da aka biya shi naira dubu dari 5 kafin ya sake ta.

Wasu majiyoyi sun ce rikin yayi sanadin mutuwar wani dan bindiga da ake kira Chirwa, kani ga Sarki Mani da matarsa, yayin da wasu mutane 3, Kabiru,, Tanimu, da Suleiman suka ji rauni, kuma suna karbar magani a Katsina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.