Isa ga babban shafi
Najeriya

Adadin Sojin Najeriya da 'yan bindiga suka hallaka a katsina ya kai 26

Adadin Sojin Najeriya da 'yan bindiga suka hallaka a yankin Jibia na jihar Katsina ya karu zuwa mutum 23 sabanin 16 da wasu jaridun Najeriya suka wallafa a jiya Lahadi. 

Wasu Sojin Najeriya a Katsina.
Wasu Sojin Najeriya a Katsina. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Kamfanin dillancin Labran Faransa AFP ya ruwaito wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta na cewa an gano gwarwakin Sojin 23 yayinda har yanzu ake ci gaba da neman wasu da suka bace.

Wani Jami'in sa kai ya shaidawa AFP cewa adadin Sojin da suka mutu ka iya zarta alkaluman da ke da su a yanzu la'akari da yadda ake ci gaba da laluben sauran jami'an ko dai a raye ko kuma a mace.

Farmakin 'yan bindigar kan dakarun Sojin Najeriyar a Katsina na zuwa dai dai lokacin da fashewar wani bomb ya hallaka yara 5 'yan gida guda duk dai a jihar ta Katsina mai fama da hare-haren 'yan bindiga.

Masana tsaro a Najeriyar na ci gaba da gargadin gwamnati kan yiwuwar 'yan bindigar wadanda suka addabi arewa maso yammacin kasar su hade kai da 'yan ta'addan Boko Haram wajen ci gaba da farmakar sassan kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.