Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun halaka sojoji 16 a Katsina

Gungun 'yan bindiga sun halaka sojojin Najeriya 16 a jihar Katsina, tare da jikkata wasu kalla 28, bayanda suka yi musu kwanton bauna.

Wasu dakarun rundunar sojin Najeriya.
Wasu dakarun rundunar sojin Najeriya. AP/Lekan Oyekanmi
Talla

Majiyoyin tsaro, sun ce maharan sun farwa dakarun sojin daga saman duwatsu ne a lokacin da suke tattakin sintiri a karamar hukumar Jibiya da misalin karfe 6 na yammacin jiya asabar.

Sai dai har yanzu rundunar sojin ba ta ce komai ba kan farmakin.

Katsina na daga cikin jihohin arewacin Najeriya masu fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga dake halaka rayukan jama’a, da kuma satar mutanen don karbar kudin fansa.

Wani rahoton cibiyar sa ido kan samar da zaman lafiya a Afrika ta Yamma, yace hare-haren ‘yan bindiga a jihar Katsina yayin sanadin mutuwar sama da mutane dubu 2, tarwatsa kauyuka 500, da kuma raba sama da mutane dubu 33 da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.