Isa ga babban shafi
Najeriya

Amurka ta damu da kisan da ake yi a arewacin Najeriya

Kasar Amurka ta yi Allah-wadai da kisan rashin hankalin da ake yi a yankin Arewacin Najeriya, inda 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka.

Shugaban Amurka Donald Trump tare da  Muhammadu Buhari na Najeriya
Shugaban Amurka Donald Trump tare da Muhammadu Buhari na Najeriya Reuters/Carlos Barria
Talla

Ofishin Jakadancin Amurka da ke Najeriya ya ce, kasar ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta dada kara kaimi wajen shawo kan tashin hankalin da ake samu da kuma hukunta duk wadanda ke da hannu a ciki.

Matsayin na Amurka ya biyo bayan kisan gillar da 'yan bindiga suka yi wa fararen hula a Jihar Kastina, abin da ya haifar da zanga-zangar lumana daga mutanen jihar.

A 'yan kwanakin nan, Najeriya ta yi fama da sabbin hare-haren 'yan bindiga da na mayakan Boko Haram, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a sassan kasar musamman a Borno da Kudancin Kaduna da Taraba da Niger da Filato da Yobe da kuma Sokoto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.