Isa ga babban shafi
Najeriya

Mun ragargaji 'yan bindiga a Zamfara da Katsina-Sojin Sama

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta ce, dakarunta na Operation Hadarin Daji sun yi nasarar kashe dimbim ‘yan bindiga a jihohin Katsina da Zamfara.

Sojojin Saman Najeriya sun yi amfani da jiragen yaki wajen kaddamar da farmaki kan 'yan bindiga a jihohin Katsina da Zamfara
Sojojin Saman Najeriya sun yi amfani da jiragen yaki wajen kaddamar da farmaki kan 'yan bindiga a jihohin Katsina da Zamfara Nigerian Monitor
Talla

Wata sanarwa da mai kula da Sashen Kafafen Yada Labarai na Rundunar, Manjo Janar John Eneche ya fitar, ta ce an kai farmakin ne da zummar kakkabe 'yan bindigar a maboyarsu.

Manjo Eneche ya ce, sun yi amfani da bayanan sirrin da suka tattara wajen zakulo maboyar tsagerun domin karya lagonsu, yana mai cewa, dakarun sun yi amfani da jiragen yaki wajen kai farmaki kan sansanoni 10 na ‘yan bindigar tare da raba su da makamansu .

Wuraren da sojojin suka kai harin sun hada da Dutsen Asolo da Birnin Kogo da ke jihar Katsina da kuma sansanin Dogo Gede da ke Dajin Kwayanbana a jihar Zamfara a cewar sanarwar da Eneche ya fitar.

Wannan na zuwa a daidai lokacin da ‘yan bindiga suka addabi wurare da dama a sassan arewacin Najeriya, inda suke kaddamar da munanan hare-haren kan mutane tare da kona gidajensu da kuma sace dukiyoyinsu baya ga yi musu yankar rago a wasu lokutan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.