Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya gana da daliban Kankara

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da daliban makarantar Sakandaren Kankara da ‘yan bindiga suka ce a daren ranar Juma’ar makon da ya gabata, 11 ga watan Disamba.

Daliban makarantar sakandaren Kankara bayan kubuta daga hannun 'yan bindiga
Daliban makarantar sakandaren Kankara bayan kubuta daga hannun 'yan bindiga RFI Hausa / Abdullahi Tanko
Talla

Yayin ganawar, Buhari ya jajantawa daliban kan irin halin fargabar da suka samu kansu bayan sace su da 'yan bindigar suka yi.

Ganawar Buhari da daliban ya biyo bayan kubutar dasu daga hannun ‘yan bindigar da gwamnati tayi a ranar Alhamis 17 ga wannan wata na Disamba, wadanda daga bisani aka kai yaran garin Katsina da safiyar ranar Juma’a.

Kafin sakin yaran dai, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fuskanci caccaka dangane da rashin ziyartar makarantar sakandaren ta Kankara bayan da aka sace daliban 343, matakin da ya fusata ‘yan Najeriya da dama.

Sai dai yayin taron manema labarai yau Juma’a, ministan yada labaran Najeriya Lai Muhammad yace kodayake Buhari bai ziyarci makarantar ta Kankara ba, shugaban ne ya jagoranci tsara dabarun da aka bi wajen ceto daliban daga garin Daura mahaifarsa, inda ya je hutun mako daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.