Isa ga babban shafi
Najeriya-Borno

Jami'an lafiya 16 sun kamu da coronavirus a Borno

Gwamnatin Borno tace jami’an lafiya 16 da aiki a jihar, sun kamu da cutar coronavirus cikin kwanaki biyu da suka gabata.

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum.
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum. RFI Hausa / Bilyaminu Yusuf
Talla

Kwamishinan lafiya a jihar ta Borno, Dakta Salisu Kwayabura ne ya sanar da kamuwar jami’an lafiyar a Maiduguri, a lokacin da yake karin bayani kan halin da ake ciki dangane da yakar annobar coronavirus da kawo yanzu ta kama jumillar mutane 75, daga cikinsu kuma ta halaka 11.

A baya bayan nan ne dai mataimakin gwamnan jihar Borno Umar Kadafur ya koka kan yadda har yanzu, akwai wani yanki na al’ummar jihar da basu yadda cewar cutar COVID-19 ko coronavirus gaskiya bace, yanayin da ya kamanta da yadda a shekarun baya wasu daga cikin mazauna jihar suka raina barazanar kungiyar Boko Haram.

Mataimakin gwamnan na Borno yace duk da karuwar yawan masu dauke da cutar coronavirus a jihar, har yanzu mutane na halartar tarukan jana’iza, gami da halartar Masallatai don Sallah a jam’i, abinda likitoci suka ce a dakatar har zuwa wani lokaci nan gaba, domin dakile yaduwar annobar murar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.