Isa ga babban shafi
Najeriya

COVID-19: Jami'an lafiya na farautar akalla mutane dubu 12 a Najeriya

Hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC, ta ce akalla mutane dubu 12 take farauta a sassan kasar, wadanda tace sun yi mu’amala da mutanen da aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar COVID-19 ko coronavirus.

Wata mata rufe da da baki da kuma hancinta a kasuwar Dutse Alhaji, dake birnin Abuja, a Najeriya.  2/5/2020.
Wata mata rufe da da baki da kuma hancinta a kasuwar Dutse Alhaji, dake birnin Abuja, a Najeriya. 2/5/2020. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Yayin zanatawa da manema labarai a karshen makon nan, shugaban hukumar ta NCDC, Dakta Chikwe Ihekweazu, yace adadin wadanda suke neman ruwa a jallo zai cigaba da karuwa, la’akari da karuwar yawan wadanda ke kamuwa da cutar bayan yi musu gwaji.

Dakta Ihekweazu, ya kuma koka kan karancin gadajen asibiti na kwantar da wadanda suka kamu da cutar coronavirus ko COVID-19 a jihohin Najeriya, yanayin da ya bayyana a matsayin barazana ga yakin da ake yi da annobar, la’akari da cewar gadaje dubu 3 da 500 kawai ake da su a fadin kasar.

A karshen watan Maris, kwamishinan lafiyar jihar Legas Farfesa Akin Aboyami, yayi gargadin cewa, yawan wadanda za su kamu da cutar ta COVID-19 a birnin ka iya kaiwa dubu 39, amma idan jama’a suka kiyaye cinkoso, adadin zai iya tsayawa a dubu 13 kawai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.