Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya za ta samu karin kudaden shiga

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan wata dokar sauye-sauyen hada-hadar man fetur tsakanin kasar da manyan kamfanonin duniya, abin da zai bai wa Najeriya damar samun karun kudaden shiga.

Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya.
Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya. REUTERS/Stringer
Talla

Sanarwar da shugaba Buhari ya bayar a birnin London, inda yanzu haka yake hutu, ta ce, shugaban ya sanya hannu kan dokar da za ta sauya yadda ake raba kudaden shigar da ake samu daga man da aka hako a cikin teku.

Sanarwar ta ce, wannan doka za ta bai wa Najeriya damar samun karin kudade daga cikin kudin da ake rabawa tsakaninta da manyan kamfanonin man duniya da ke hakar mai a gabar ruwan kasar.

Ya zuwa yanzu dai babu tabbacin ko wannan sabuwar dokar za ta fara aiki nan take, ko kuma za ta bada damar tattaunawa da kamfanonin man domin sake yarjeniyoyin da suka kulla.

Ofishin shugaba Buhari ya ce, sabuwar dokar za ta bai wa Najeriya damar samun akalla Dala biliyan 1 da rabi na karin kudin shiga daga shekarar 2021.

Kamfanonin da Najeriya ke aiki tare da su sun hada da Exxon Mobil da Chevron Eni da Total da kuma CNOOC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.