Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya amince da tsawaita rufe kan iyakokin Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shirin ci gaba da rufe kan iyakokin kasar har gaba da ranar 31 ga watan Janairun shekara mai zuwa.

Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya.
Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Babban Jami’in Hukumar Kwastam da ke Kula da sashen bincike da kuma sa ido, David Dimka ya sanar da haka a wasikar da ya rubuta wa jami’an hukumar da ke jihohi da kuma kan iyakokin kasar.

Rufe iyakokin na zuwa ne watanni 3 kacal bayan Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwancin bai daya tsakanin kasashen Afirka.

Matakin rufe kan iyakokin na ci gaba da haddasa cece-kuce, inda wasu ke lale marhabin da shi, yayin da wasu ke kokawa saboda a ganinsu, matakin shi ne ummul-haba’isin tashin farashin kayayyaki a kasuwannin Najeriya da suka hada da abinci.

A yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, Dr.Kasim Kurfi, masanin tattalin arziki a Najeriya, ya bayyana cewa, matakin rufe kan iyakoki na din-din-din ba zai taimaka ba wajen bunkasar tattalin arzikin kasa.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da muka yi da Kasim Kurfi wanda ya yi fashin baki na musamman kan rufe iyakokin Najeriya.

03:38

Dr. Kasim Kurfi kan matakin rufe iyakokin Najeriya

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.