Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta dakile fasakaurin kayayyakin da suka zarta na triliyan 2

Kusan watanni uku bayan rufe kan iyakokinta na kan tudu da ta yi, gwamnatin Najeriya ta sanar da kwace haramtattun kayayyakin da darajarsu ta kai naira triliyan 2 da biliyan 300, wadanda aka yi yunkurin fasakaurin shigar da su cikin kasar.

Wani sashi na Seme, kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin.
Wani sashi na Seme, kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin. REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo
Talla

Kakakin hadin gwiwar jami’an tsaron dake aikin sintirin kan iyakokin Najeriyar na kan tudu, Joseph Attah ya ce kayayyakin da suka yi nasarar kwacewa sun hada da bindigogi, alburusai, ababen hawa, magunguna, shinkafa, da kuma tankunan man fetur.

Attah ya kuma ce, jami’an tsaron hadin gwiwar da suka hada da na Kwastam, shige dafice, ‘yan sanda da sojoji, sun kame bakin-haure 203 dake kokarin satar shiga Najeriya, sai kuma masu safarar mutane guda 8.

Ranar 20 ga watan Agustan da ya gabata, shugaban Najeriya Muhd Buhari, ya bada umarnin rufe iyakokin kasar na kan tudu, na wucin gadi, domin kawo karshen matsalar fasakaurin haramtattun kayayyaki cikin kasar, daga kasashe makwabta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.