Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya hana kudaden shigo da abinci cikin Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci Babban Bankin Kasar, CBN da ya dakatar da bayar da kudaden waje ga masu shigo da abinci cikin kasar domin bunkasa harkar noma a cikin gida.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP
Talla

Kodayake shugaba Buhari bai yi karin bayani ba, amma rahotanni na cewa, tuni babban bankin na CBN ya daina bayar da kudaden ketare ga masu shigo da shinkafa da man-ja da man-gyada da nama da ganyayyaki da kajin gona da kwai da talatalo da kifin gwangwani da tumatur da dai sauran nau’ukan abinci har guda 41.

Shugaba Buhari ya ce, lura da ci gaban da ake samu wajen samar da albarkatun gona da kuma cikakken tsaron abinci a Najeriya, babu bukatar shigo da wasu kayayyakin abinci cikin kasar.

Shugaban ya kara da cewa, za a ci gaba da tattalin asusun ajiyar kudaden waje na Najeriya domin fadada tattalin arzikin kasar, yana mai cewa, ba a tanadi asusun ba domin ci gaba da dogaro kan shigo da abinci daga kasashen katare.

Shugaban ya ce, jihohin Kebbi da Ogun da Lagos da Jigawa da Ebonyi da Kano sun amfana da wannan tsarin na gwamnatin Najeriya, inda suka bunkasa noman shinkafarsu.

Najariya wadda ke kan gaba wajen karfin tattalin arzaiki a nahiyar Afrika, ta dagara da shigo da abinci daga kasashen ketare domin ciyar da al’umarta da yawanta ya kai kusan miliyan 200.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.