Isa ga babban shafi
Najeriya

Har yanzu kungiyar IPOB haramtacciya ce - Ebonyi

Gwamnatin Ebonyi da ke kudancin Najeriya ta gargadi ‘ya’yan kungiyar IPOB da ke jihar da su kaucewa shirya gudanar da wani taro ko zanga-zanga.

Wasu 'ya'yan haramtacciyar kungiyar IPOB yayin zanga-zanga a garin Aba, dake kudu maso gabashin Najeriya. 18/11/ 2015.
Wasu 'ya'yan haramtacciyar kungiyar IPOB yayin zanga-zanga a garin Aba, dake kudu maso gabashin Najeriya. 18/11/ 2015. AFP Photo/Pius Utomi Ekpei
Talla

Sakataren gwamnatin Ebonyi Kenneth Ugbala, da kuma Kenneth Uhuo, kwamishinan yada labaran jihar ne suka yi gargadin cikin sanarwar hadin gwiwar da suka fitar a Abakaliki, babban birnin jihar.

Sanarwar ta jaddada cewa har yanzu kungiyar ta IPOB haramtacciya ce a Najeriya, dan haka ba ta da hurumin gudanar da dukkanin wasu al’amuran da suka shafi, taruka ko kuma zanga-zanga.

Gargadin ya zo ne mako guda bayan da ‘ya’yan haramtacciyar kungiyar ta IPOB uka gudanar da wata zanga-zanga a Abakaliki don nuna kyama ga shirin tsugunar da makiyaya na RUGA da gwamnatin Najeriya ta dakatar, da kuma karin manufofin gwamnatin.

Cikin watan Janairu na shekarar 2018, babbar kotun tarayyar Najeriya da ke Abuja ta yi watsi da karar shugabannin kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra, da ke bukatar kotun ta soke ayyana su da gwamnatin Najeriya ta yi a matsayin ‘yan ta’adda.

Yayin yanke hukuncin Mai shari’ah Abdul Kafarati, ya ce gwamnatin Najeriya ta cike dukkanin ka’aidojin da ya kamata, kafin mika wa kotun bukatar haramta kungiyar ta IPOB, dan haka babu inda aka sabawa doka.

A watan Satumba na shekarar 2017, Gwamnonin Yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya suka bayyana haramta kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra karkashin jagorancin Nnamdi Kanu.

Matakin da ya zo a dai dai lokacin da rikici ke neman girmama a wasu yankunan kasar duk dai kan bukatar kafa kasar ta Biafra.

A waccan lokacin gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi ya ce sun cimma matsayar ne tare da shugabannin Yankin da Yan Majalisun Tarayya da suka fito daga Yankin da kuma shugabanin kungiyar kabilar Igbo ta Ohaneze.

Kafin daukar matakin, rundunar sojin Najeriya ceta soma sanar da haramta kungiyar wadda ta bayyana a matsayin ta yan ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.