Isa ga babban shafi
Najeriya

A kyale mutane su zabi wanda suke so - Buhari

Fadar Gwamnatin Najeriya ta gargadi ‘yan takarar jam’iyyyar APC mai mulki a jihohin da zaben Gwamnoni da na ‘yan Majalisu bai kammala ba da cewa, shugaban kasar Muhammadu Buhari, ba zai yi katsalandan a zabukan da za a yi a ranar Asabar mai zuwa ba, 23 ga watan Maris.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Fadar gwamnatin Najeriyar ta kuma kara da gargadin ‘yan siyasar da ke furta kalaman tunzara jama’a domin tayar da rikici yayin zabukan da ke tafe.

Sanawar da Gwamnati ta fitar a ranar Lahadi, ta shawarci ‘yan takarar jam’iyyar APC musamman na kujerun Gwamna, da su yi watsi da tunanin cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tilastawa hukumar INEC sauya alkalumman kuri’u dan taimaka musu wajen lashe zabukan.

A maimakon tunanin tafka magudi, fadar gwamnatin Najeriyar ta shawarci shugabannin jam’iyyar APC da ke jihohi 6 da za a karasa zaben Gwamnonin, da su jajirce wajen neman amincewar mutane ta sahihiyar hanya domin kada musu kuri’a a ranar Asabar.

Tuni dai hukumar zaben Najeriya INEC ta shirya gudanar da taro a ranar Talata, kan zaben kujerun Gwamnonin a Adamawa, Kano, Benue, Plateau, Bauchi da kuma Sokoto.

Ina sa ran INEC za ta gana da hukumomin tsaro kan tunatar da su kan gudanar da ayyukansu na tabbatar da tsaro kadai yayin zabukan, ba tare da yiwa masu kada kuri’a da jami’an INEC katsalandan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.