Isa ga babban shafi
NAJERIYA-MDD

"Hare-haren Boko Haram sun karu a Najeriya"

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke Kula da Kaurar Baki ta ce, an samu karuwar hare-haren kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya a cikin watanni 3 da suka gabata, abin da ya raba mutane dubu 59 da 200 da muhallansu.

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram
Wasu daga cikin mayakan Boko Haram pmnewsnigeria
Talla

Hukumar da ke da cibiya a Geneva ta ce, karuwar hare-haren na nuna yadda kungiyar ke kara farfadowa da kuma jefa rayuwar mazauna jihohin Borno da Yobe da Adamawa cikin hadari.

Jami’in hukumar a Najeriya, Frantz Celestin ya ce, daga watan Nuwamba zuwa yanzu sun karbi mutane dubu 59 da 200 da suka tsere daga gidajensu, abin da ba su taba gani ba a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Hukumar ta ce, yanayin hazon da ake samu tsakanin watannin Nuwamba zuwa Maris, na yin illa ga ayyukan soji wajen fuskantar mayakan da ke kai hare-hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.