Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotuna sun yanke hukunci masu cin karo kan makomar APC a Zamfara

Wata babbar kotu da ke Gusau a Zamfara, ta yanke hukuncin tabbatar da zaben fidda gwanin Jam’iyyar APC a jihar, wanda ya gudana a ranakun 3 da 7 ga watan Oktoban shekarar 2018.

Harabar babbar kotun Nigeria da ke Abuja.
Harabar babbar kotun Nigeria da ke Abuja. Premium Times Nigeria
Talla

Kotun wanda ke karkashin mai Shari’a Muhammad Bello Shinkafi, ta kuma umarci hukumar zaben Najeriya INEC, ta amince da zaben fidda gwanin na APC da ya shafi mukamin gwamna, ‘yan majalisun dokokin tarayya da kuma na dokokin jihar.

Zalika kotun ta haramta sauya sunayen wadanda suka yi nasara a zaben fidda gwanin.

Sai dai wata babbar Kotu da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa hukumar INEC tana da ikon kin karbar 'yan takarar jam'iyyar APC a zabukan na jihar Zamfara.

Jaridar the Nation da ke Najeriya ta rawaito cewa, yayin gabatar da hukuncin a wannan Juma'a 25 ga watan Janairu, mai shari'a Ijeoma Ojukwu, ta ce rashin 'yan takarar APC a Zamfara ba laifin hukumar INEC bane, laifi ne na jam'iyyar kanta, saboda gaza kammala zabukanta cikin wa'adin da aka tsara domin zabukan fidda gwanin.

Ranar 10 ga watan Oktoban bara, INEC ta ce, jam’iyyar APC mai mulki ba tada dan takara a matakin jihar Zamfara yayin zabukan 2019, saboda gazawarta wajen kammala zabukan fidda ‘gwani, cikin wa’adin da hukumar ta INEC ta debawa daukacin jam’iyyun siyasar Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.