Isa ga babban shafi
Najeriya

"Ya kamata INEC ta haramta wa APC takara a Zamfara"

Jam’iyyun adawa a jihar Zamfara da ke tarayyar Najeriya, sun bukaci hukumar zabe, INEC da ta shelanta cewa, jam’iyyar APC mai mulki a jihar ba ta da ‘yan takara a zabuka masu zuwa, saboda a cewarsu jam’iyyar ta gaza gudanar da zabukan fid da gwani kafin ranar 7 ga watan Oktoba kamar yadda ka’idojin zabe suka shata.

Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari ya yi ikirarin kammala zaben fid da gwani
Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari ya yi ikirarin kammala zaben fid da gwani RFI Hausa
Talla

A hirarsa da sashen hausa na RFI, Alhaji Sa’idu Muhammad Dansadau, shugaban Jam’iyyar National Rescue Movement wadda suke kira da Jam’iyyar Ceton Al’umma na kasa kuma dan takarar gwamna a jihar, ya ce tuni suka sanar da hukumar zabe a hukumance dangane da haka.

Dansadau ya ce, dokokin Najeriya sun bukaci haramta wa wata jam’iyya shiga takarar zabe muddin ta gaza gudanar da zaben fid da gwani.

Kuna iya latsa alamar sauti da ke kasa don sauraron muryar Alhaji Dansadau.

01:00

"Ya kamata INEC ta haramta wa APC takara a Zamfara"

Sai dai gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari ya yi ikirarin kammala gudanar da zaben na fid da gwanin jamiyyar APC kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito.

Amma tawagar uwar jam’iyya ta kasa da aka aika don sanya ido a zaben, ta ce, babu wani zaben fid da gwani da aka gudanar a Zamfara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.