Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan APC za su kalubalanci zaben fid da gwani a Kano

'Ya’yan jam'iyyar APC 60 da suka nemi tikitin tsayawa takara a zaben fid da gwani na jihar Kano sun lashi takobin kalubalantar sakamakon zabukan na fid da gwani da aka gudanar.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya samu tikitin tsayawa takaran gwamna
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya samu tikitin tsayawa takaran gwamna Daily Post
Talla

Sanata Isa Zarewa da ke magana a madadin ‘yan takaran 60 ya bayyana cewa, abin da ya faru a Kano ya yi hannun riga da manufar jam’iyyar APC, in da ya ce, a matsayinsu na wadanda aka kafa jam’iyyar da su, ba za su fice daga cikinta ba, amma za su tabbatar cewa, an yi abin da ya dace don kare martabar jam’iyyar.

Sanata Zarewa ya ce, “dukkanin wadanda suka yi takarar neman tikitin Majalisar Tarayya da ta Jiha da kuma aka take hakkokinsu ta hanyar rashin gudanar da zaben fid da gwanin, sannan kuma aka kirkiri sakamako, sun hadu wuri guda don tattauna mafita. Mun dauki matakin ne ba don komai ba, sai don makomar jam’iyyar a matakin jiha da tarayya”

Zarewa ya kara da cewa, tuni suka kafa wani kwamiti da zai gabatar da batun ga shugabancin jam’iyyar da kuma shugaban kasa, sannan kuma ya duba yiwuwar daukan matakin shari’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.