Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya bada umarnin gurfanar da Babachir Lawal

Mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya ce, shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin gurfanar da tsohon Sakataren Gwamnatin Kasar, Babachir Lawal saboda zargin sa da handame kudaden da aka ware domin agaza wa ‘yan gudun hijirar Boko Haram.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Najeriya, Babachir Lawal.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Najeriya, Babachir Lawal. AFP
Talla

Osinbajo ya ce, shugaba Buhari ya bukaci Hukumomin Yaki da Cin Hanci da Rashwa na kasar da su shirya tuhumar Lawal wanda aka sauke daga mukaminsa a ranar 31 ga watan Oktoban shekarar 2017.

Wannan na zuwa ne bayan caccakar da ake yi wa gwamnatin Buhari na jan-kafa wajen gurfanar da Lawal, yayin da rahotanni ke cewa, yana cikin ‘yan sahun gaba da ke yi wa Buhari yakin neman sake zaben sa.

Har ila yau, shugaba Buhari ya bada umarnin gurfanar da tsohon Datekta Janar na Hukumar Leken Asirin kasar, Ayodele Oke wanda shi ma ake zargi da aikata almundahana.

An samu tarin dukiyoyi a wani gida da ke unguwar Ikoyi a jihar Legas, kudaden da ake danganta wa da Mr. Oke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.