Isa ga babban shafi
Najeriya

Ba a cimma matsaya kan sabon tsarin biyan albashi ba - Ngige

Ministan Kwadagon Najeriya Chris Nigige, ya ce gwamnati bata cimma matsaya da kungiyar kwadagon kasar kan sabon tsarin biyan mafi karancin albashi ba, kamar yadda wasu kafafen yada labarai ke yadawa.

Ministan Kwadagon Najeriya Chris Ngige.
Ministan Kwadagon Najeriya Chris Ngige. Daily Post
Talla

Yayin wata zantawa da manem labarai a Abuja, Ngige, ya ce har yanzu bangarorin da batun ya shafa na kan tattaunawa, kafin cimma matsayar sabon tsarin albashin.

Ministan ya musanta rahotannin da ke cewa, an cimma matsayar tsarin biyan mafi karancin albashi na naira dubu 30.

Ngige, yayi karin bayanin cewa, kungiyar kwadago ce ta gabatar da kudurin biyan ma'aikata mafi karancin albashi na naira dubu 30, yayinda gwamnatin Najeriya ta gabatar da tayin naira dubu 24, su kuma gwamnonin jihohi, suka yi tayin naira dubu 20, don haka a cewar ministan, gabatar da tayin naira dubu 30 da bangaren ‘yan kwadago na gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu suka yi bayan cimma matsaya tsakaninsu, ba ya nufin cewa gwamnatin Najeriya ta amince da tayin kai tsaye.

Sai dai cikin wata sanarwar da kungiyar kwadagon ta fitar ta yi watsi da bayanan ministan tare da bayyana mamaki dangane da ikirarin da yayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.