Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiyar kwadagon Najeriya ta soma yajin aikin gama gari

Yau Alhamis ma’aikatan Najeriya suka tsunduma cikin yajin aikin gama gari na ‘sai baba ta gani’ saboda gazawar gwamnati dangane da shirin amincewa da kuma biyan karin albashin da suke bukata.

Wasu daga cikin 'ya'yan kungiyar kwadagon Najeriya.
Wasu daga cikin 'ya'yan kungiyar kwadagon Najeriya. The Guardian Nigeria
Talla

Yayin ganawa da manema labarai a jiya Laraba, shugaban kungiyar kwadagon Najeriya NLC Ayuba Waba, yace yajin aikin zai shafi ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni, abinda zai sanya rufe makarantu da bankuna, ma’aikatuda kuma gidajen mai.

Yunkurin gwamnatin kasar na kaucewa yajin aikin wajen ganawa da shugabannin kungiyar jiya yaci tura, saboda rashin amincewa da bayanan da Ministan kwadagon kasar Chris Ngige yayi musu.

Yayin ganawar da Nigige yayi da kungiyar Kwadagon, yayi alkawarin cewa, kwamitin da aka dorawa alhakin warware takaddamar, zai sake zama a ranar 4 ga watan Oktoban 2018, domin fayyace matakin karshe da ake ciki, dangane da cimma matsaya kan batun na karin albashi.

Alkawarin na Ministan kwadagon Najeriya dai ya gaza yin tasiri wajen dakatar da yajin aikin, domin kuwa kungiyar kwadagon kasar ta ce ba zata janye hukuncin da ta yanke ba, bayan karewar wa’adin makwanni biyu da ta baiwa gwamnatin Najeriya.

Kwamrade Nasir Kabir wanda yayi magana a madadin kungiyar kwadagon ta Najeriya ya shaidawa sashin Hausa na RFI cewa, tattaunawarsu da Ministan kwadagon kasar ta tashi ne baram-baram.

00:28

Kwamrade Nasir Kabir - Ma'aikatan Najeriya sun soma yajin aikin gama gari

Garba Aliyu

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.