Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 579 sun mutu a rikicin makiyaya a Najeriya

Akalla mutane 579 suka rasa rayukansu tsakanin watan Janairu zuwa Juni na wannan shekarar sakamakon rikicin makiyaya da manoma a jihohi 4 na Najeriya.

Gawarwakin wasu mutane da suka mutu a sanadiyar rikicin makiyaya da manoma a jihar Benue
Gawarwakin wasu mutane da suka mutu a sanadiyar rikicin makiyaya da manoma a jihar Benue Pius Utomi Ekpei/AFP
Talla

Wani bincike da Jaridar Daily Trust ta gudanar ya ce, an samu asarar rayukan ne a jihohin arewa ta tsakiya da suka hada da Benue da Filato da Kogi da kuma Nasarawa.

Kimanin mutane 503 aka kashe a cikin watanni shida, da suka hada da manoma da matafiya da kuma wasu mabiya addinin Kirista a daukacin wadannan jihohin hudu a cikin wannan shekara.

Kazalika an hallaka makiyaya 76 a cikin watannin 6 a Benue da Nasarawa da kuma Filato, amma babu makiyayi guda da aka kashe a Kogi a wannan lokaci.

Har ila yau, an yi awon gaba da shanu 98, in da aka kashe tare da raunata wasu shanun a jihar Nasarawa kadai a cikin watanni shidan farko a wannan shekara.

Binciken na zuwa ne a yayin da wasu barayin shahu suka hallaka mutane 26 a cikin kwanaki biyu akan iyakokin jihohin Sokoto da Zamfara kamar yadda Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasar ta sanar a ranar Laraba.

Mai magana da yawun hukumar, Suleiman Kadir, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, barayin sun kuma kona gidaje tare da sace shanu.

Kadir ya ce, akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutu ya karu nan gaba, lura da cewa ana ci gaba da neman wasu da suka bace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.