Isa ga babban shafi
Najeriya

An hana zirga-zirgar shanu a kudancin Najeriya

Gwamnonin yankin kudu maso gabashin Najeriya sun gudanar da wani taro a jihar Enugu a karshen mako, in da suka tsayar da shawarar hana zirga-zirgar shanu a yankin baki daya bisa fargabar hare-haren makiyaya.

Wikimedia Commons/Fabrizio Demartis
Talla

Gwamnonin sun kuma bukaci ganawa da hafsoshin tsaron Najeriya bisa fagabar yaduwar kashe-kashen da makiyaya ke yi a yankin.

A cewar gwamnonin, suna dari-dari kan cewar, matsalar kashe-kashen da aka gani a jihohin Filato da Taraba da Zamfara da wasu sassa na kasar, za ta shafi yankin nasu.

Kazalika gwamnonin sun jaddada matayinsu na watsi da shirin samar da wuraren kiwo, in da suke cewa, gwamnatin tarayya na da masaniya cewa, babu wadatattun filaye a yankinsu.

Wannan na zuwa ne kwana guda da fadar shugaban kasar ta roki ‘yan Najeriya da sauran kasashen duniya da su kauce wa furta kalaman da ka iya rura rikicin manoma da makiyaya a kasar.

Fadar ta ce, shugaba Muhammadu Buhari, ba mai nuna banbancin kabila ko kuma addini ba ne a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.