Isa ga babban shafi
Najeriya

Matasa sun far wa gidan gwamnatin jihar Filato

Wasu matasa sun gudanar da zanga-zangar nuna bacin-rai kan hare-haren da aka kaddamar a kauyukan karamar hukumar Barikin Ladi da ke jihar Filato ta Najeriya, in da suka afka wa gidan gwamnati tare da farfasa kofofin gilasai da kuma lalata motocin da ke harabar gidan gwamnatin.

Yadda wasu daga cikin masu zanga-zangar suka haura shingen gidan gwamnatin jihar Filato
Yadda wasu daga cikin masu zanga-zangar suka haura shingen gidan gwamnatin jihar Filato Daily Trust/Nigeria
Talla

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, reshen jihar Filato ce ta bai wa daukacin mabiya addinin Kirista umarnin fitowa don gudanar da gagarumar zanga-zanga a karkashin jagoranci iyaye mata da kuma wasu matasa.

Jami’an tsaro sun yi kokarin lallashin masu zanga-zangar amma haka ya ci tura, lamarin da ya sa suka yi harbi a iska don tarwatsa su.

Rahotanni na cewa, da fari matasan sun yi alkawarin gudanar da zanga-zangar lumana don nuna bacin-ransu kan rikcin wanda ya lakume rayuka da dama, amma daga bisani zanga-zangar ta dauki wani sabon salo.

Gwamnatin Filato ta ce, adadin mutanen da suka mutu ya zarce 200, yayin da ake ta daukar matakan ganin an shawo kan tashin hankalin, ko da dai kungiyar CAN ta ce, adadin ya zarce haka.

Bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo na daga cikin wadanda suka ziyarci jihar don jajanta wa al’ummarta.

A bangare guda, rundunar sojin Najeriya ta gabatar da wasu mutane da ta kama da ake zargin cewar suna da hannu wajen kazamin tashin hankalin a jihar Filato.

Tuni shugaba kasar  Buhari ya gana da shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da na Majalisar Wakilai Yakubu Dogara game da wannan rikici da ke barazana ga zaman lafiya a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.