Isa ga babban shafi
Najeriya

EFCC ta fara bincikar jiga jigan PDP a Kano da Sokoto

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta gurfanar da wasu jiga jigan jam’iyyar PDP a jihohin Sokoto da Kano gabanta, bisa zarginsu da almundahanar kudade a lokacin gudanar da zaben shekarar 2015 da ta gabata.

Hukumar EFCC ta fara binciken wasu manyan jam'iyyar PDP kan zaben 2015.
Hukumar EFCC ta fara binciken wasu manyan jam'iyyar PDP kan zaben 2015. RFI / Pierre Moussart
Talla

A jihar Kano dai hukumar ta sanar da gayyato mutane uku da suka hada da Ambasada Aminu Wali tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, da Malam Ibrahim Shekarau tsohon gwamnan jihar, bisa zarginsu da almundahanar kudi naira miliyan 900.

Sai dai daga bisani hukumar ta bayyana sakin su, bisa sharadin zasu sake kai kansu gabanta don ci gaba da masa tambayoyi.

A Sokoto kuwa hukumar ta EFCC ta bayyana kama tsohon mataimakin gwamnan jihar Mukhtari Shagari da Sanata Abdallah Wali da wasu mutane da dama.

Sauran wadanda hukumar ta gurfanar, sun hada da Ibrahim Gidado da Nasiru Bafarawa da Ibrahim Milgoma.

Hukumar dai na tuhumar su ne da halarta kudaden haramun da suka kai naira miliyan 500 da suka karba daga tsohuwar ministar man Najeriya Diezani Allison Maduekwe.

Sai dai Alhaji Yusuf Dingyadi, dan Majalisar zartaswa na jam’iyyar PDP a Sokoto, ya ce binciken hukumar ta EFCC, bita-da-kullin siyasa ne.

00:14

Alhaji Yusuf Dingyadi dan Majalisar zartaswa na jam’iyyar PDP a Sokoto.

Faruk Yabo

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.