Isa ga babban shafi
Najeriya

Obasanjo zai amsa tambaya kan Dala biliyan 16- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo na da wasu tambayoyi da zai amsa game da kashe Dala biliyan 16 da aka ware don gudanar da aikin samar da wutar lantarki a zamanin mulkinsa.

Shugaba Muhammadu Buhari tare da Olusegun Obasanjo
Shugaba Muhammadu Buhari tare da Olusegun Obasanjo nationaldailyng.com
Talla

Shugaba Buhari ya fadi haka ne a a lokacin da yake karbar wata kungiyar magoya bayansa karkashin jagorancin shugaban hukumar Kwastam, Hameed Ali a fadarsa da ke birnin Abuja a yau Talata.

Duk da dai Buhari bai ambaci sunan Obasanjo karara ba, amma ya dika ayar tambayar cewa, "Ina aka samu wutar lantarki bayan wani tsohon shugaban kasa ya yi ikirarin kashe Dala biliyan 16 akan aikin samar da wutar".

A lokacin mulkin Obasanjo ne aka kaddamar da wani gagarumin aikin samar da lantarki a Najeriya, yayin da masu sa ido da kungiyoyin fareran hula suka bayyana aikin a matsayin barnatar da kudaden talakawa.

Ko a shekarar 2008, sai da Majalisar Wakilan kasar ta bayyana Dala biliyan 16 din da aka kashe a mulkin na Obasanjo a matsayin wata babbar barnar dukiya.

A shekarar 2016, kungiyar SERAP da ke sa ido kan tattalin arziki ta bukaci mukaddashin alkalin-alkalai na kasar a wancan lokaci, Walter Onnogheb da ya kafa wani kwamiti da zai binciki zarge-zargen rashawa dangane da kashe Dala biliyan 16 a gwamnatin Obasanjo.

Obasanjo dai na cikin wadanda suka taka gagarumar rawa wajen ganin Buhari ya samu nasara a zaben 2015 da aka gudanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.