Isa ga babban shafi
Najeriya

Ya kamata 'yan jam'iyyar PDP su kwaikwayi Ibrahim Mantu - APC

Yayinda da Siyasar Najeriya ke da yin dumi, jam’iyyar APC mai mulki, ta bukaci ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP, su yi koyi da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijan kasar Ibrahim Mantu, wajen bayyana laifukan da suka yi wa ‘yan Najeriya tare da neman afuwa.

Shugaban jam'iyyar APC mau mulki a Najeriya, Cif John Odigie-Oyegun.
Shugaban jam'iyyar APC mau mulki a Najeriya, Cif John Odigie-Oyegun. Daily Post
Talla

Kiran na APC ya zo ne bayan da Sanata Ibrahim Mantu ya bayyana cewa tabbas a zamaninsu, ya taimakawa jam’iyyarsa ta PDP wajen magudi a zabe, ta hanyar, bayar da cin hanci domin tsohe duk wani korafi da ka iya tasowa.

A lokacin da Mantu ya ke bayyana haka, ya ce yayi nadama akan aikata kura-kuran, wadanda ya sha alwashin gyarawa.

A cewar jam’iyya mai mulki ta APC, tsabar rashin gaskiya da ke damun PDP ne ya tilastawa shugabancin jam’iyyar fitowa fili ta nemi afuwar ‘yan Najeriya, bisa kura-kuran da ta ce ta tafka a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.