Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Borno ta rufe makarantun da ke fadin jihar

Gwamnatin Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya mai fama da rikicin Boko Haram ta rufe makarantun kwana da ke jihar har sai baba ta gani.

Rufe makarantun na da nasaba da sace 'yan matan makarantar Chibok da na Dapchi da Boko Haram ta yi
Rufe makarantun na da nasaba da sace 'yan matan makarantar Chibok da na Dapchi da Boko Haram ta yi REUTERS/Ola Lanre
Talla

Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta ce, matakin ba zai shafi makarantun kwanar da ke birnin Maiduguri da kuma garin Biu ba.

Rufe makarantun na da nasaba da sace sama da ‘yan matan makarantar Chibok 200 da Boko Haram ta yi a cikin watan Afrilun shekarar 2014 da kuma wanda ya faru na baya-bayan nan a jihar Yobe, in da kungiyar ta sace daliban makarantar Dapchi 110 duk da cewa ta dawo da 105 daga cikinsu.

Mayakan Boko Haram dai sun sha kaddamar da farmaki a makarantun Boko da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya tun lokacin da hare-harensu ya yi kamari a shekarar 2009.

Asusun Kula da Ilimin kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce, sama da malaman makarantun boko dubu 2 da 296 ne suka rasa rayukansu, yayin da aka lalata makarantu dubu 1 da 400 a sanadiyar rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.