Akwai kyakkyawan fata kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya - IMF
Asusun bada lamuni na Duniya IMF, yace hasashensa ya nuna cewar Najeriya zata samu cigaban tattalin arzikin ta na matsakaicin lokaci.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahotan asusun ya bayyana cewa akwai alamu mai kyau bna bunkasa tattalin arzikin kasar duk da yan matsalolin da ake fuskanta, sakamakon sauye sauyen da gwamnatin kasar ke aiwatar wa, wanda asusun yace ya zama wajibi a gaggauta su.
Asusun tace tashin farashin mai zai taimakawa kasar sosai, ganin yadda kwanciyar hankalin da aka samu a Yankin da ake hako man ya dore.
Sai dai IMF ya ce yayin da tattalin arzikin Najeriya ke farfadowa sannu a hankali, har yanzu akwai mutane da dama da ke cikin halin matsi a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu