Isa ga babban shafi
Najeriya

An tura jiragen yaki 100 don neman daliban Dapchi

Rundunar sojin saman Najeriya, ta aike da jiragen yaki 100, domin neman daliban makarantar ‘yan mata ta Dapchi 110 da aka sace a ranar 19 ga watan Fabarairu.

Jirgin sojin saman Najeriya.
Jirgin sojin saman Najeriya. naij.com
Talla

Ministan yada labaran Najeriya, Lai Muhammad ya ce a Litinin kadai jiragen yaki 20 ne suka yi shawagi tsawon awanni 200 zuwa daren ranar.

A ranar Talata, babban hafsan sojin saman kasar Air Marshal Sadik Abubakar, ya koma zuwa jihar Yobe domin lura da jagorancin neman daliban da kansa, wadanda ake zargin mayakan Boko Haram da sacewa.

A ranar 15 ga watan Maris mai zuwa, ake sa ran kwamitin da gwamnatin Najeriya ta kafa kan sace daliban makarantar ta Dapchi, ya mika rahoton bincikensa.

A ranar Talata mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan sha’anin tsaro, Janar Babagana Munguno, ya sanar da aikewa da Karin jiragen yaki 80 zuwa yankin arewa maso gabashin kasar domin karawa jiragen yaki 20 da aka fara aikawa neman daliban makarantar ‘yan matan ta Dapchi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.