Isa ga babban shafi
Najeriya

"Mun janye dakarunmu kafin sace 'yan matan Dapchi"

Rundunar Sojin Najeriya ta bakin Ofishin Kwamandan Operation Lafiya Dole da ke yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar, Manjo Janar Rogers Ibe Nicholas, ta amince da janye dakarunta daga garin Dapchi na Yobe kafin mayakan Boko Haram su sace ‘yan matan makarantar Sakandaren garin.

Wasu daga cikin sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar
Wasu daga cikin sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar REUTERS/Tim Cocks
Talla

Rundunar ta ce, ta mika ragamar kula da tsaron yankin ga jami’an ‘yan sanda da ke jihar.

Mai magana da yawun Nicholas, Kanar Onyema Nwachukwu ya ce, bai kamata a dora laifin sace ‘yan matan akan sojoji ba saboda sun mika ragamar tsaro cikin kwanciyar hankali da lumana ga ‘yan sanda.

Nwachukwu ya kara da cewa, an janye sojojin ne don girke su a garin Kanama da ke kan iyakar Najeriya da Nijar don yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram da ke kai hare-hare kan sansanin soji a yankin.

Sai dai a bangare guda, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe, Sumonu AbdulMaliki ya musanta ikirarin sojin na mika musu ragamar tsaron Dapchi a hannunsu.

Rundunar ta ce, ba za ta bata lokaci ba wajen jayayyaya da gwamnatin jihar Yobe kan sace ‘yan matan saboda ta karkata hankalinta kan yadda za ta ceto daliban daga hannun mayakan.

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar cewa, ‘yan mata 110 ne mayakan na Boko Haram suka sace bayan sun kai farmaki a ranar Litinin ta makon jiya, al’amarin da ya razana iyayen yaran, musamman idan aka yi la’akari da ‘yan matan Chibok da Boko Haram ta sace a shekarar 2014 a Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.