Isa ga babban shafi
Najeriya

Makiyaya sun ci gaba da kai mana hari a Benue- Ortom

Gwamnan jihar Benue da ke Najeriya, Samuel Ortom ya ce, al’ummarsa na ci gaba da fuskantar hare-haren makiyaya da ya bayyana su a matsayin ‘yan ta’adda.

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya ce, Buhari ya ki ziyartar jiharsu duk da kisan da aka yi wa al'ummarsa a rikicin makiyaya
Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya ce, Buhari ya ki ziyartar jiharsu duk da kisan da aka yi wa al'ummarsa a rikicin makiyaya naij.com
Talla

Mr. Ortom ya bayyana haka ne a yayin zantawarsa da wakiliyar sashen Faransanci na RFI Bineta Diagne a birnin Makurdi, fadar gwamnatin jihar.

Gwamnan ya ce, “Bayan jana’izar mutane 73 da aka kashe a farkon wannan shekara, mun ci gaba da fuskantar wasu hare-hare daga wadannan sojojin haya, mu muna kiran su da suna ‘gungun makiyaya ‘yan ta’adda’’ a Najeriya.”

Gwamnan ya kara da cewa “Babban abin taikaici, hatta ma jami’an tsaro ba su tsira daga wadannan mahara ba, ‘yan sanda sun nuna gazawarsu, sannan kuma har yanzu sojojin da ake zance ba su fara aiki ba.”

00:40

Muryar Gwamna Samuel Ortom na Benue

Mr. Ortom ya bukaci a cafke maharan don hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

A bangare guda, gwamnan ya ce, ba za a gudanar da yakin neman zabe a jihar ba matukar aka gaza shawo kan rikicin, yayin da ya yi korafin cewa, shugaba Buhari bai ziyarce su ba duk da kisan da aka yi wa al'ummarsa.

Alkaluman kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International na cewa akalla mutane 168 ne suka rasa rayukansu a jihar daga watan janairu zuwa yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.