Rikicin makiyaya: Sojin Najeriya na dab da isa jihohi 6
Rundunar sojin Najeriya ta ce, za ta tura dakarunta jihohin Benue da Taraba da Kaduna da Niger da Kogi da kuma Nasarawa domin kawo karshen rikicin da ake samu tsakanin makiyaya da manoma wanda ke haddasa asarar dimbin rayuka. Matakin na zuwa ne kasa da sa’oi 24 bayan alkawarin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi a lokacin da ya ziyarci jihar Nasarawa na kare lafiyar mutanen da ke tsakiyar Najeriya da kuma fadin kasar baki daya. Manjo Janar David Ahmadu, kwamandan ayyuka na musamman ya ce, za a fara tura sojojin ne daga ranar 15 ga wannan wata na Fabarairu. Wakilinmu daga Abuja, Muhammad Kabir Yusuf ya hada mana rahoto.
Wallafawa ranar:
Rikicin makiyaya: Sojin Najeriya na dab da isa jihohi 6
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu