Isa ga babban shafi
Najeriya

Gudunmawar masu kishin Najeriya ta zama tilas - Dan Sadau

Wasu ‘yan siyasa a Najeriya sun bukaci dukkanin masu kishin kasar da su jajirce, domin bada gudunmawar kan matsalolin da ke addabar kasar.

Sanata Sa'idu Dan Sadau, kuma shugaban jam'iyyar NRM.
Sanata Sa'idu Dan Sadau, kuma shugaban jam'iyyar NRM. Blueprint
Talla

Sanata Sa’idu dan Sadau, tsohon dan majalisar dattawan Najeriya yana daga cikin jiga-jigan ‘yan siyasar kasar da suke wannan kira.

Yayin zantawarsa da Sashin Hausa na RFI, Sanata dan Sadau, ya ce nuna kishin kasa domin magance matsalolin da ke addabar ta ya zama tilas, idan aka yi la’akari da halin da talakawan Najeriya masu yawan gaske ke ciki, na rashin tsaro sakamakon tashe tashen hankula, rikicin kabilanci da addini, da kuma satar mutane ana garkuwa da su domin karbar kudi.

Sanata Saidu Dansadau, a yanzu shi ne shugaban sabuwar Jam’iyyar NRM ya ce abin damuwa ne matuka a ce a halin yanzu talaka yana kokarin tsira da rayuwarsa ce a maimakon dukiyarsa.

00:40

Gudunmawar masu kishin Najeriya ta zama tilas - Dan Sadau

Bashir Ibrahim Idris

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.