Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan Najeriya na bukukuwan Kirsimeti cikin wahalar man Fetir

Yayin da ‘yan Najeriya suka bi sahun takwarorinsu na duniya domin bukukuwan zagayowar ranar Kirsimeti, Mutane da daman na ci gaba da dogon layin neman Fetir da ke wahalar samu a sassan kasar.

'Yan Najeriya na bukukuwan Kirsimeti a layin Man Fetir
'Yan Najeriya na bukukuwan Kirsimeti a layin Man Fetir AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Duban motoci da sauran ababben hawa sun yi cuncurundo a gidanjen man tun da sanyin safiyar wannan ranar ta Kirsimeti a fadin kasar, yayin da akasarin gidajen man a rufe wadanda suka bude kuma sun ninka kudin fetirin. Wannan kuwa duk da ikirarin da Kamfanin NNPC ke yi cewa yana da yawan man da zai gamsar da 'yan kasar.

A ranar juma’ar da ta gabata, NNPC ya ce ya kara adadin man da ya ke fitarwa a ranar daga lita miliyan 35 zuwa 80. Kamfanin ya ce yana aiki tare da manyan kamfanonin ‘yan kasuwa irinsu Total da Forte Oil da Oando da MRS da Conoil da NIPCO wajen dakon man daga Lagos zuwa sauran sassan kasar.

Sai dai wannan kokari na NNPC bai yi tasirin ko rage wahalhalun jama’a ba, inda ko a birnin Tarayyar kasar Abuja gidajen man da dama na fama da karanci fetir. Wannan matsalar dai ya hana kristoci zuwa wajen ibadarsu.

Kazalika akasarin mutane da suke tafiye-tafiye a wannan lokaci na Kirsimeti sun gaza biyan kudadden motar da aka tsawala, lamarin da ya tilastawa da dama fasa tafiyar.

Rahotannin jaridun Najeriya sun ce ana siyar da lita guda na fetir daga 350 zuwa 600 al’amari da ya haifar da karin kudadden motar da takaita zirga-zirga a wannan lokaci na bukukuwan Kirsimeti da kuma karshan shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.