Isa ga babban shafi
Najeriya

Jami'an tsaro sun gano ma'aikatar sarrafa makamai a Najeriya

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta sanar da gano wata masana’antar kera makamai a kauyen Shenagu da ke yankin Zuba kusa da Abuja babban birnin kasar. Hakan dai na zuwa ne kwana guda bayan kama wasu tarin makamai da aka shigo da su kasar ta tashar jirgin ruwa da ke Lagos.

Gano masana'antar sarrafa makaman dai na zuwa ne kwana guda bayan kame wasu tarin makamai da aka shigo da su kasar, lamarin da ka iya zama barazana ga zaman lafiyar Kasar.
Gano masana'antar sarrafa makaman dai na zuwa ne kwana guda bayan kame wasu tarin makamai da aka shigo da su kasar, lamarin da ka iya zama barazana ga zaman lafiyar Kasar. Reuters
Talla

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Abuja Sadiq Bello ya shaidawa taron manema labarai cewa suna tsare da wasu mutane uku da ake zargin suna da hannu cikin ayyukan masana’antar.

A cewar Sadiq Bello bayan hukumar 'yansanda ta kammala bincike za kuma ta mika batun gaban kotu don daukar matakin daya dace.

Najeriya dai yanzu haka na fama da matsalar tsaro tun bayan barkewar rikicin kungiyar nan mai fafutukar kafa kasar Biafra lamarin da ke ci gaba da sanya razani a zukatan da dama daga al'ummar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.