Kwastam ta kama makamai 1,100 a Najeriya
Hukumar Kwastam a Najeriya ta sanar da kama wasu bindigogi 1,100 da aka shiga da su kasar ba tare da izini ba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban hukumar Kanar Hameed Ali ya ce anyi safarar makaman ne daga kasar Turkiya.
Wannan na daga cikin matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta ganin irin yadda matsalar tsaro da aikata laifufuka ya addabe ta.
Wannan shine karo na Uku da ake kwace makamai da ake shigo da su kasar daga ketare a watanni 9 wanda ya kawo adadin makamai 2,201 da kwastam ta gano.
Shugaban Hukumar ya ce sun kaddamar da bincike domin gano masu hannu a shigar da makamai kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu