Isa ga babban shafi
Najeriya-Legas

Hukumar Kwastam ta kame tarin makamai a birnin Legas

Hukumar yaki da fasa kaurin kayayyaki ta Najeriya, da aka fi sani da Kastam, ta samu nasarar kame tarin makamai a birnin Legas.

Makaman da hukumar Kastam ta Najeriya ta kama a birnin Legas
Makaman da hukumar Kastam ta Najeriya ta kama a birnin Legas
Talla

Rahotanni sun ce yawan makaman sun kai a iya rabawa bataliya guda ta rundunar soji.

Majiya daga hukumar hana fasakaurin ta ce, manyan bindigogi masu aman wuta akalla 661 jami’ai suka gano, boye cikin wasu akwatuna 46.

Shugaban hukumar Kastam din ta Najeriya, Kanal Hameed Ali mai ritaya, ya ce, jami’an hukumar sun gano, tarin akwatunan da aka boye ne cikin wani akwatin dakon kaya mai tsawon kafa 40, wadda aka karkata akalarta zuwa yankin Apapa da ke jihar Legas, cikin wata babbar mota.

Kanal Hameed Ali ya ce ana tsare da mutane uku da ake zargi da shigo da makaman, yayinda ake cigaba da gudanar da bincike.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.